in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake kai harin kunar bakin wake a kasar Somaliya
2009-12-04 17:51:40 cri

Tun daga shekarar 1991, ana ta yin yaki a kasar Somaliya, kuma ana da rikice-rikace da yawa cikin tarayyar gwamnati, har ma an wargaza gwamnati sau da dama. Ban da haka kuma, ana ta samu hare-hare, tare da matsalar 'yan fashin jirgin ruwan teku, halin da ake ciki a kasar Somaliya yana yi tsananta sosai. A farkon shekarar bana, an yi babban zabe na kasar Somaliya a Djibouti, Mr. Sharif ya zama shugaban kasar, kuma ya kafa sabuwar gwamnatin wucin gadi. Amma sabuwar gwamnati ba ta iya kwanta da halin da ake ciki ba, dakaru mai adawa da gwamnati na "al-Shabab" ya ce zai hambarad da gwamnatin Sharif.

Kafin haka kuma, Sharif shugaban kasar Somaliya ya taba yin kira ga kasashen Turai da dama da su cika alkawarinsu na ba da taimako domin kara karfin gwamnatin wucin gadi ta kasar Somaliya. Wasu kwararru sun yi shawarwari cewa, ya kamata kasar Somaliya ta kafa tushen tsarin kasa kan gwamnatoci na kauyuka, da garurruka da unguwoyi, daga baya ta kafa gwamnatocin yankuna, a karshe ta hada gwamnatin yankuna ta kafa tarayyar gwamnatin kasa domin gudanar da harkokin kasa tare. Amma akwai masu bincike sun yi nuni da cewa, ainihin jama'ar kasar Somaliya ya lalata sosai sakamakon yaki, ya kamata su kasa mai da hankali ga moriyar kabilu, maimakon haka su yi kokari domin kafa wata dinkuwar kasa. [Musa Guo]


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China