in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake kai harin kunar bakin wake a kasar Somaliya
2009-12-04 17:51:40 cri

Bayan da shugaba Sheikh Sharif Sheikh Ahmad na gwamnatin wucin gadi ta kasar Somaliya ya sami wannan labari, ya ce, wannan harin kunar bakin wake shi ne bala'in kasar. Game da haka, kungiyar tarayyar Afirka ta ce ba za ta daina goyon baya ga jama'ar kasar Somaliya wajen shimfida zaman lafiya ba. Ban da haka kuma, majalisar dinkin duniya, da kasar Amurka, da kungiyar tarayyar Turai, da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa sun bayarn da wata sanarwa cewa, kasashen duniya za su ci gaba da goyon bayan gwamnatin wucin gadi ta kasar Somaliya. A ran 3 ga wata, Mr. Ban Ki-moon, babban sakataren MDD ya bayar da sanarwa cewa, wannan harin zai sa kasashen duniya su kara sanin ya kamata a kara ba da tabbacin tsaro ga hukumomin kasar Somaliya da kungiyar wakilan kungiayr tarayyar Afirka da ke Somaliya.

Wannan shi ne harin kunar bakin wake na biyu da aka yi a kasar Somaliya a shekarar da muke ciki. A watan Yuni na shekarar bana, ministan tsaro na gwamnatin wucin gadi ta kasar ya mutu cikin wani harin kunar bakin wake. Ana tsamanin kungiyar "al-Shabab" ta yi yawancin hare-hare, kuma an ce wannan kungiyar ita ce karamar kungiyar "al-Qaeda" a kasar Somaliya. Ko da yake har zuwa yanzu babu wani ko kungiya da ta dauki nauyin aikata wannan hari, amma wadanda suka shaida abin da ya faru da idanunsu, sun ce, dan kunar bakin wake shi ne mamban kungiayr "al-Shabab".

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China