in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake kai harin kunar bakin wake a kasar Somaliya
2009-12-04 17:51:40 cri

Ran 3 ga wata da safe, an yi harin kunar bakin waken da ya hallaka a kalla mutane 17 a wani otel da ke Mogadishu babban birnin kasar, ciki har da ministoci 3 na gwamnatin wucin gadi ta kasar, wasu mutane fiye da 200 sun jikkata. Masu bincike suna ganin cewa, wannan harin ta'adda ya kara yiwa gwamnatin wucin gadi ta kasar matsala, halin da ake ciki a kasar Somaliya ya kara tsananta.

An bayyana cewa, bam din ya tashi ne a otel na Shamow da ke wata unguwa da ke karkashin ikon gwamnatin kasar. Yayin da ake dana bam din, wasu manyan jami'ai na gwamnati suna yin bikin yaye dalibai. Mutane da yawa sun mutu ko jikkata, an rasa ministan kiwon lafiya, da ministan ba da ilmi, da ministan al'adu na kasar a harin. Ban da haka kuma, 'yan jaridu biyu na kasar Somaliya sun mutu.

Wadanda suka shaida abin da ya faru da idanunsu, sun ce, wata mace ta shiga otel ta dana bam din cikin mutane. Ministan watsa labaru na kasar ya fayyace cewa, wannan hari shi ne wani harin kunar bakin wake, wani namiji ya dana bam din, ya sa tufafin mace kuma ya sa likaf. An bayyana cewa, ba a dauki matakan tsaro sosai a wannan biki ba, dukkan 'yan gadi na ministoci suna waje.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China