in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sauye-sauyen yanayi yana yin mummunan illa ga tattalin arziki da zaman al'ummar Afirka
2009-11-30 20:34:48 cri

Kasashen Afirka suna ganin cewa, ya kamata kasashe masu ci gaba su biya diyya gakasashen Afirka kan hasararsu sakamakon sauye-sauyen yanayi, kuma yayin da ake yin shawarwari wajen tinkarar sauye-sauyen yanayi da kafa tsarin duniya, dole ne a tsaya tsayin daka kan ka'idar "dauki matsaya daya amma nauyi daban daban", mai da bunkasuwa mai dorewa, da aikin rage masifar talauci, da shirin raya kasa cikin sabon karni a kasashen Afirka a matsayi mai muhimmanci, a sa'i daya kuma, kasashen Afirka su bukaci kasashe masu ci gaba su cika alkawarinsu na ba da taimakon kudi da fasahohi ga kasashen Afirka a zahiri.

Amma, wasu kasashe masu tasowa ba su cika alkawarinsu ba. Daga wajen fannin rage fitar da abubuwan da ke dumama yanayi, yawancin kasashe masu tasowa ba su yi isashen aiki da "yarjejeniyar Kyoto" ta tsara, kuma ba su dauki matakai a zahiri wajen ba da taimakon kudi da fasahohi ba.

Kafofin watsa labaru na kasashen Afirka sun yi nuni da cewa, sauye-sauyen yanayi shi ne batun muhalli, kuma shi ne batun bunkasuwa, kasashen Afirka suna kokarin tinkarar wannan matsala, ya kamata kasashe masu tasowa su kara ba da taimako ga kasashen Afirka a zahiri domin inganta karfinsu wajen tinkarar sauye-sauyen yanayi. [Musa Guo]


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China