in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sauye-sauyen yanayi yana yin mummunan illa ga tattalin arziki da zaman al'ummar Afirka
2009-11-30 20:34:48 cri

A kwanakin baya, rukunin Bakoxin, wani shahararren kamfanin aikin hidima kan hada-hadar kudi ya bayar da wani sakamakon nazari cewa, idan ba a iya warware matsalar sauye-sauyen yanayi, watakila a cikin shekaru masu zuwa da dama, za ta hadasa hasara mai yawan kashi 15 cikin 100 na GDP na kasashen Afirka a ko wace shekara. Haka kuma a kwanakin baya, bankin duniya ya bayar da wani rahoto cewa, kasashen Afirka suna fuskantar da matsalolin tabarbarewar muhalli da sauye-sauyen yanayi.

Madam Marianne Fay kwararriyar masanin ilmin tattalin arziki ta farko mai kula da harkokin bunkasuwa mai dorewa ta bankin duniya ta yi nuni da cewa, kudin da kasashen Afirka suka samu daga aikin gona ya kai kashi 30 cikin 100 na GDP nasu, amma sauye-sauyen yanayi zai yi mummunan illa ga aikin gona na manoma na kasashen Afirka. Madam Fay ta ce, bisa nazarin da aka yi, ya zuwa shekarar 2080, kashi 9 zuwa kashi 20 cikin 100 na filayen Afirka za su karancin inganci sosai. Yanzu kashi 86 cikin 100 na filayen da ke kudu na Sahara suan da matsalar karancin ruwa, idan ba a iya inganta karfin aikin gona, za a sami matsala wajen samar da isasshen hatsi a Afirka.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China