in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sauye-sauyen yanayi yana yin mummunan illa ga tattalin arziki da zaman al'ummar Afirka
2009-11-30 20:34:48 cri

Bisa sakamakon kididdigar da kwamitin musamman tsakanin gwamnatocin kasashe na MDD ya yi, a cikin shekaru 8 da suka wuce, sakamakon sauye-sauyen yanayi, kasashe da dama na Afirka sun sami matsalar karancin ruwan sama. A farkon shekarar bana, kwamitin tattalin arzikin Afirka na MDD ya yi kiyasin cewa, a shekarar 2009, yawan mutanen Afirka da ba su da isasshen abubuwan gina jiki ya kai kusan miliyan 200.

Ban da haka kuma, wasu kasashen Afirka suna da matsalar karancin makamashi. Labaran bankin duniya ya nuna cewa, a cikin shekaru 25 masu zuwa, yawan mazaunai a garurruka da birane zai karu miliyan 300, bukatun makamashi da ake da su a Afirka zai karu sosai.

Sakamakon sauye-sauyen yanayi, yawan makamashin ruwan da ake da su a Afirka yana raguwa. A cikin shekarun baya, yawan ruwan koguna yana raguwa, wannan ya haddasa yawan wutalantarkin da aka samu daga karfin ruwa ya ragu sosai.

Yanzu kasashen Afirka sun riga sun ganin mummunan illa da sauye-sauyen yanayi ya yi, kuma suna kokarin shiga yukurin shawarwarin sauye-sauyen yanayi da kafa tsarin duniya. Yawancin kasashen Afirka sun riga sun sa hannu kan "yarjejeniyar sauye-sauyen yanayi ta MDD", da "yarjejeniyar Kyoto", kuma suna kokarin neman ra'ayi iri daya da kuma kara taka muhimmiyar rawa cikin shwarwarin sauye-sauyen yanayi na duniya.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China