in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zazzabin cizon sauro na ci gaba da caza kan mutanen Afirka sosai
2009-11-24 14:03:25 cri

A ganin wani jami'in aususun yanar gizo na yaki da zazzabin cizon sauro na Afirka, a cikin shekaru 4 da suka wuce, sabbin manyan tsare-tsare kan yaki da zazzabin cizon sauro, da kulawar da kasashen duniya ke nunawa matuka kan batun, da kuma goyon bayan da gwamnatocin kasashen da ke fama da wannan mummunan ciwo suke nunawa sun sanya mutanen da suka fi gazawa a harkoki daban daban su samu karin hanyoyin yin rigakafi da shawo kan zazzabin cizon sauro. Amma tilas ne a ci gaba da horar da dimbin masu nazarin ciwon a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara, ta haka kasashen da suka fi fama da ciwon za su iya tsara shirin nazari da kansu.

Kada mu manta, a sakamakon rashin isashen kudi da sauran dalilai, kasashen da ke fi fuskantar matsalar yaduwar zazzabin cizon sauro, wadanda yawancinsu kasashe ne na Afirka, su kan kasa samun iasassun na'urori da magungunan yin rigakafi da shawo kan ciwon. Musamman ma a yankunan karkara da ke cikin wadannan kasashe, zazzabin cizon sauro ya fi yin illa a wurin. (Tasallah)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China