in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zazzabin cizon sauro na ci gaba da caza kan mutanen Afirka sosai
2009-11-24 14:03:25 cri

Ko da yake ana iya yin rigakafi da kuma shawo kan zazzabin cizon sauro a halin yanzu, amma ya zuwa yanzu wannan mummunan ciwo na kasancewa daya daga cikin manyan munanan cututtuka da suke caza kan kasashen duniya. A kwanan baya, masu nazari da masu aikin kiwon lafiya da jami'ai masu kula da kiwon lafiya da masu kula da yanayin zamantakewar al'umma fiye da dubu 2 da suka fito daga sassa daban daban na duniya sun taru a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya, da zummar halartar babban taron Pan-Afirka kan yin kirar daukar matakai a tsakanin bangarori daban daban domin shawo kan zazzabin cizon sauro a karo na 5. Wadanda suka halarci taron na tsawon kwanaki 5 sun yi kira ga kasashen duniya da su dauki hakikanin matakai, da inganta nazarin magunguna da na'urorin yin rigakafi da shawo kan zazzabin cizon sauro da kuma kyautata manufofin da abin ya shafa.

Bisa kididdigar da aka samu, an ce, a ko wace shekara, mutane miliyan dari 3 zuwa miliyan dari 5 na kamuwa da zazzabin cizon sauro a duk duniya gaba daya, yayin da wasu miliyan 1 da dubu dari 5 zuwa miliyan 3 ke mutuwa a sakamakon ciwon, ciki kuma har da wadanda yawansu ya kai kashi 90 cikin dari a kasashen Afirka. Abu mafi bakin ciki shi ne a cikin wadannan mutanen da suka mutu a sakamakon zazzabin cizon sauro a Afirka, wadanda da yawansu ya kai kashi 85 cikin dari su yara ne da tsawon shekarunsu bai wuce 5 a duniya ba.

Daya daga cikin muhimman makasudai na shirya taron da aka yi a Nairobi shi ne inganta karfin kasashen Afirka na yaki da zazzabin cizon sauro da kuma taimaka musu wajen kyautata manufofi da matakan yin rigakafi da shawo kan ciwon.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China