in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zazzabin cizon sauro na ci gaba da caza kan mutanen Afirka sosai
2009-11-24 14:03:25 cri

A ganin wadanda suka halarci taron, ko da yake bayan da aka yi irin wannan taro a shekarar 2005, kasashen duniya sun samu ci gaba da yawa wajen yaki da zazzabin cizon sauro, duk da haka, kasashe da yawa na Afirka sun gamu da matsala wajen tabbatar da wani muhimmin batun da ke cikin manufar bunkasuwa da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara a shekarar 2000, wato hana yaduwar zazzabin cizon sauro da kuma shawo kansa. Watakila da kyar su tabbatar da manufar da Hukumar Kiwon Lafiya ta Kasa da Kasa wato WHO ta tsara, wato za a rage yawan wadanda suka mutu a sakamakon ciwon da rabi a shekarar 2010.

Duk da haka, wasu kasashen Afirka sun samu kyawawan fasahohi wajen yaki da zazzabin cizon sauro. Alal misali, a kasar Rwanda, zazzabin cizon sauro ya fi kawo wa mazauna wurin barazanar mutuwa yau shekaru 5 da suka wuce, amma bayan da aka rarraba gidajen sauro da kuma horar da masu aikin kiwon lafiya da ke aiki a unguwanni, a shekarun baya, an rage yawan wadanda suke mutuwa a sakamakon ciwon da kashi 60 cikin dari bisa na da. A tsibirin Zanzibar na kasar Tanzania, bayan da aka rarraba dimbin gidajen sauro a farkon shekarar 2006 tare kuma da kashe sauro da maganin kashe kwari, yanzu a wurin, an rage yawan yaran da shekarunsu ba su wuce 2 a duniya ba, da ke kamuwa da ciwon sauro da kashi 95 cikin dari bisa na da.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China