in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Fuxin da ke samar da kwal yana kokarin canja hanyar ci gaban tattalin arziki
2009-11-24 13:41:12 cri

Bisa labarin da aka bayar, an ce, ya zuwa shekara ta 2008, yawan manyan masana'antu da ke birnin Fuxin ya kai fiye da dari 3, kuma yawan adadin kudin da suke samarwa a kowace shekara daya ya kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 24, wato ya ninka sau 4.5 bisa na shekara ta 2001. Sakamakon haka, yanzu ya riga ya zama birnin da ke kunshe da jerin masana'antun samar da injuna masu aiki da mai irin na musamman da na kere-kere, kuma wadannan masana'antu suna goyon bayan kokarin canja tsarin tattalin arzikin birnin Fuxin.

Mr. Gao Zhengmin, shugaban kwamitin harkokin tattalin arzikin birnin Fuxin ya ce, a cikin shekaru 8 da aka yi ana canja tsarin tattalin arziki a birnin, inganci da karfin tattalin arziki na birnin Fuxin ya samu kyautatuwa wajen yin gasa a kasuwanni, kuma tsarin kayayyakin da ake samarwa da tsarin sana'o'in wannan birni sun kuma samu kyautatuwa kamar yadda ake fata. Mr. Gao ya ce, "A shekara ta 2001, sana'a ta farko, sana'ar aikin gona ta kai kashi 40 cikin kashi dari, tare da sana'a ta biyu, wato sana'ar kere-kere ta kai kashi 30 cikin kashi dari, sannan sana'a ta uku, wato sana'ar ba da hidima ta kai kashi 30 cikin dari. Amma ya zuwa shekara ta 2008, an canja wadannan adadi, wato yanzu sana'a ta farko ta kai kashi 22.3 cikin dari, sana'a ta biyu ta kai kashi 40 cikin dari tare da sana'a ta uku ta kai kashi 37.7 cikin dari. Bugu da kari kuma, a da, masana'antu da kamfanonin da suke da nasaba da kwal da wutar lantarki sun fi yawa a birnin Fuxin, amma yanzu lokacin da ake sauya tsarin sana'o'i, masana'antun kere-kere suna samun karfi, kuma suna samun ci gaba cikin sauri. Yanzu, an riga an samu hanyar neman ci gaba bisa makamashin da ake da shi da muhimman kayayyakin da ake samarwa, kuma an kafa masana'antun da suke samar da kwatankwacin kayayyaki a sansani daya domin za su iya dogara da juna wajen neman ci gaba."

Bayan da aka yi shekaru 8 ana neman hanyoyin canja tsarin tattalin arziki, ya zuwa yanzu, birnin Fuxin ya riga ya samu kyakkyawan sakamako a mataki na farko wajen canja tsarin tattalin arzikinsa. Mr. Liu Wenqi, shugaban kwamitin yin gyare-gyare da ci gaban birnin Fuxin ya bayyana cewa, a nan gaba, za a kara yin amfani da karfin da har yanzu ba a yi amfani da shi ba tukuna wajen raya tattalin arziki. Farar hula kuma za su ji dadin zaman rayuwarsu. Mr. Liu ya ce, "Bisa shirin da muka tsara, za mu yi amfani da shekaru 15 wajen cimma dukkan burinmu a fannin tattalin arziki. Sakamakon haka, matsakaicin GDP na birnin Fuxin zai kai ko wuce matsakacin GDP na duk kasar Sin, kuma zai kai matsakaicin GDP na lardin Liaoning. Haka kuma, za mu iya cimma burinmu na kyautata muhallinmu da tabbatar da ci gaban sana'o'inmu mai dorewa. Zaman rayuwar jama'a ma za ta iya samun kyautatuwa, har ma za a iya samun jituwa a tsakanin al'ummomi daban daban kamar yadda ya kamata." (Sanusi Chen)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China