in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Fuxin da ke samar da kwal yana kokarin canja hanyar ci gaban tattalin arziki
2009-11-24 13:41:12 cri

Birnin Fuxin da ya shahara sosai a kasar Sin wajen fitar da kwal yana arewa maso gabashin kasar. An riga an yi fiye da shekaru dari ana hakar kwal. Amma tun daga shekaru 80 na karnin da ya gabata, birnin Fuxin da ke dogara kan sana'ar kwal wajen raya tattalin arziki ya soma shiga mawuyacin hali sakamakon raguwar yawan adanannun kwal, sannan yawan kudin da aka kashe ya yi ta karuwa wajen hakar kwal. A watan Disamba na shekara ta 2001, gwamnatin kasar Sin ta sanya birnin Fuxin da ya zama birni mai arzikin albarkatu na farko wajen canja hanyar neman ci gaban tattalin arziki. A cikin shekaru 8 da suka gabata, birnin Fuxin ya yi kokari kuma ya yi gwaje-gwajen canja hanyoyin ci gaban tattalin arziki.

Game da sabon tsarin tattalin arzikin da gwamnatin birnin Fuxin ta tsara, Mr. Liu Wenqi, shugaban kwamitin yin gyare-gyare da raya birnin Fuxin ya ce, "Da farko dai, samarwa da kuma sarrafa amfanin gona. Birninmu yana dogara da sansanin aikin gona, sabo da haka, mun samar da sabbin guraban aikin yi ga wadanda suka rasa aikin yi a kamfanonin kwal. Mun riga mun samu sakamako mai kyau. Sannan yin kokarin samar da sabon makamashi. Fuxin birni ne mai arzikin albarkatun iska. Sabo da haka, muna da shirin kafa wani sansanin samar da wutar lantarki mai aiki da karfin iska, wato wannan sansani zai iya samar da wutar lantarki da yawansa ya kai kilowatts miliyan 3 a kowace shekara. Bugu da kari kuma, muna kokarin neman makamashin hasken rana da dai sauransu."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China