in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Fuxin da ke samar da kwal yana kokarin canja hanyar ci gaban tattalin arziki
2009-11-24 13:41:12 cri

Bayan da aka yi nazari kan halin da birnin Fuxin ke ciki wajen raya sabbin sana'o'in tattalin arziki, a shekara ta 2008, gwamnatin birnin Fuxin ta karfafa da kuma kyautata tsarin tattalin arziki, kuma ta tsai da kudurin raya sana'o'in jima da masana'antun da ke samar da injuna masu aiki da wani irin mai ko ruwa da na samar da katako. Birnin Fuxin zai yi amfani da shekaru 3 ko 5 domin kokarin kafa masana'antu dari 2 ko dari 3 bisa wannan sabon tsarin raya tattalin arziki. Bisa wannan tsari, za a kafa wani sansanin jima mafi girma da sansanin samar da kayan gida da na samar da injuna masu aiki da wani irin mai ko ruwa mafi girma a arewacin kasar Sin, kuma za su iya zama muhimman sana'o'in da ke tallafawa tattalin arzikin birnin Fuxin.

A ran 1 ga watan Oktoba na shekarar da muke ciki, a gun bikin duba faretin soja da aka yi a nan birnin Beijing, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya dauki mota kirar Hongqi, wato Jar Tuta da kasar Sin ta kera da kanta domin duba faretin sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin. Abin da jama'ar birnin Fuxin suke jin alfahari shi ne injin canja karfin motar da shugaba Hu ya dauka shi ne kayan da aka kera a sansanin samar da injuna masu aiki da mai irin na musamman. Ya kasance tamkar wata muhimmiyar sana'ar da birnin Fuxin ke mai da hankali sosai a kai wajen raya ta, sansanin samar da injuna masu aiki da mai irin na musamman yana jawo dimbin kamfanoni wadanda suke da jari da jami'o'i da hukumomin nazarin fasahohin zamani da su zuba jari da fasahohin zamani a cikin wannan sansani. Sabo da haka, sansanin ya zama wata muhimmiyar unguwar da take kan gaba da takwarorinsa a kasar Sin wajen mallakar fasahohin zamani a sana'ar samar da injuna masu aiki da mai irin na musamman. Mr. Wang Wenxin wanda ke jagorantar wannan sansani ya ce, "Muna kokarin kafa masana'antu kimanin dari 6 cikin sansanin, kuma yawan kudaden da za a iya samarwa a wannan sansani zai kai kudin Sin yuan biliyan 100 a cikin shekaru 3 zuwa 5 masu zuwa. Ya zuwa yanzu, yawan masana'antun da aka kafa a cikin sansanin, kuma sun riga sun soma aiki ya kai 13, a waje daya, yawan masana'antun da za su shiga sansanin zai kai 72, wadanda za su zuba jarin da yawansa zai kai kudin Sin yuan biliyan 5. Yanzu, an riga an soma gina ayyuka 55 na samar da injuna masu aiki da mai irin na musamman."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China