
Lubabatu:Tarihin wasannin Olympics na nakasassu tarihi ne na wayin kai wajen kulawa da rayukan dan Adam. Nuna girmamawa ga nakasassu da kulawa da su da taimaka musu muhimman alamu ne na cigaban zamantakewar al'umma. Kuma gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ta samar da wani sabon dakali ga nakasassu na duk duniya wajen cimma burinsu. Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayyana cewa, Lawal:"Za mu yi amfani da gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing wajen ci gaba da yada ruhun jin kai, da dukufa kan kiyaye muradun nakasassu, da ba da tabbaci ga nakasassu wajen sa hannu a cikin harkokin zaman al'umma cikin adalci, da kuma more sakamako mai kyau da aka samu a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma. Kuma na yi imanin cewa, a matsayinta na wani dakalin kara fahimtar nakasassu na kasashe daban daban da kuma kara zumuncin da ke tsakaninsu, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing za ta samar da dukiyar tunani mai daraja sosai ga sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu na duniya."
Lubabatu: A yau da dare, An kashe wutar wasannin Olympics na nakasassu na Beijing. A yau da dare kuma, an mika wa birnin London na kasar Birtaniya ikon shirya wasannin, haka kuma a yau da dare, mun alkawarta, domin duniya daya, da kuma mafarki guda, bari mu sake saduwa a wasannin Olympics na birnin London na shekara ta 2012. To, masu sauraro, sai bayan shekaru hudu masu zuwa.
Lawal:Masu sauraro, abin da kuka saurara dazun nan shirin musamman ne da muka tsara domin bikin rufe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin. Kuma mun nuna muku godiya da saurarar shirin, da haka Lubabatu da Lawal daga nan Beijing ke cewa a kasance lafiya. (Jamila Zhou,Tasallah, Musa, Bilkisu, Kande) 1 2 3 4 5 6
|