Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-17 22:23:45    
An rufe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing

cri

Lubabatu:Bisa kididdigar da aka yi an ce, tun daga shekarar 2001, an gudanar da ayyukan yin gyare-gyaren na'urori marasa shinge fiye da dubu 14 a nan birnin Beijing, yawan na'urori marasa shinge da aka kafa ya yi daidai kamar jimlarsu da aka kafa gaba daya a shekaru 20 da suka wuce.

Lawal:Wasannin Olympics na nakasassu na Beijing, wani gagarumin wasanni ne ga duk duniya wajen yin cudanya ta hanyar lumana, ya karfafa yin cudanya da juna, da sada zumunta. Shugaban kungiyar wakilai ta wasannin Olympics na nakasassu ta kasar Iran, kuma mataimakin shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na duniya Qafur Kargari ya jaddada cewar, "A ganina, wasannin Olympics na nakasassu wani gagarumin wasanni ne wajen nuna jin kai a duk duniya, nakasassu daga wurare daban daban na duniya sun taru a gun wasannin. Kazalika kuma, shirya wasannin na karfafa nuna fahimtar juna da yin cudanya a tsakanin jama'a daga kabilu, da kasashe daban daban. Wasannin Olympics na nakasassu, da wasannin Olympics dukkansu su ne gagaruman wasanni na zaman lafiya da sada zumunta, sun kawo wa duk 'dan Adam albishir na nuna kirki ga juna, da yin nesa da yaki, da zubar da jini, da kuma rikici."

Lubabatu:Wasannin Olympics na nakasassu na Beijing na da ma'ana sosai: 'Yan wasa nakasassu fiye da 4000 daga kasashe da shiyyoyi 147 sun shiga wasannin, kuma yawan kasashe da yankuna da suka shiga wasannin ya zama na farko a tarihin wasannin Olympic na nakasassu, kuma a karo na farko an yi amfani da tsarin bayar da labarai da alamun hannu, don samar da sauki ga nakasassu a wajen kallon wasanni, ban da wannan kuma, an kafa bangon tunawa da yarjejeniyar ikon nakasassu, wannan ne karo na farko da aka kafa bangon tunawa da ke mayar da yarjejeniyar M.D.D. a matsayin babban takensa. Lallai, dukkansu sun kara tasirin da wasannin Olympics na nakasassu ke kawowa, kuma sun samar da kyakkyawan fata kan wasannin Olympics.

1 2 3 4 5 6