Lubabatu:Beijing ya yi ayyuka da yawa wajen samar da ayyukan yau da kullum da zirga-zirga marasa shinge domin neman cimma nasarar gudanar da gasar Olympic ta nakasassu. Alal misali, an kafa na'urorin daukar mutane da alamun hanyoyi marasa shinge cikin tashoshin jirgin kasa da ke tafiya a karkashin kasa, an kyautata asibiti da otel-otel domin ba da tabbacin marasa shinge, ban da haka kuma, an shimfida hanyoyin da makafi ke iya tafiya da na'urorin daukar mutane a cikin wurare masu yawon shakatawa. Masu aikin sa kai miliyan 1.7 daga kasashe da yankuna 27 sun yi kokarin samar da hidima ga nakasassu daga fannoni dabam daban, wannan ya nuna kokarin da Beijing ya yi domin cimma tunaninsa na "yin ficewa, da haduwa, da morewa".
Mr. Philip Craven shugaban kwamitin wasannin Olympic ta nakasassu na duniya ya ce, Lawal:"Dukkan ayyukan da Beijing ya yi sun biya bukatun kwamitin shirya gasar Olympic ta nakasassu na duniya, kuma sun fi kyau daga wasu fannoni. Idan ka je kauyen gasar Olympic ta nakasassu ka yi hira tare da 'yan wasa, ko ka duba su kawai, za ka iya fahimtar cewa, suna jin dadin ayyuka marasa shinge, da abinci, da zirga-zirga."
Lawal:Jama'a masu sauraro, maraba da sauraren shirinmu na musamman da gidan rediyon kasar Sin ke gabatar muku game da bikin rufe wasannin Olympics na nakasassu na Beijing.
Lubabatu:An kawo karshen wasannin Olympics na nakasassu a nan birnin Beijing, amma tasirin da wasannin ke kawowa zai kasance cikin tsawon lokaci. Shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na duniya Philip Craven na ganin cewa, shirya wasannin Olympics na nakasassu na shekarar 2008 na Beijing cikin nasara, zai bayar da kayayyaki masu daraja da dama ga duk kasar Sin.
Lawal:"Da farko dai, wasannin Olympics na nakasassu na Beijing ya bayar da yawan dakuna, da filayen motsa jiki, har ma da cibiyoyin warkar da nakasassu da aka gina musamman. Na biyu, wasannin Olympics na nakasassu na Beijing zai sa kaimi ga ayyukan kafa na'urori marasa shinge a birnin Beijing, har ma a birane na duk kasar Sin, ta yadda za a kara bayar da sauki ga tafiyar nakasassu."
1 2 3 4 5 6
|