Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-17 22:23:45    
An rufe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing

cri

Lawal:A gun bikin, magajin birnin Beijing Guo Jinlong ya mayar da tutar kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya ga shugaban kwamitin Philip Craven, daga baya kuma Mr. Craven ya mika tutar ga Boris Johnson, magajin birnin London wanda zai shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2012. Wannan ya alamanta cewa, a hukunce birnin London ya sami iznin shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu.

Lubabatu:A filin wasan motsa jiki na kasar Sin, wato "Shekar Tsuntsu". 'Yan kallo sama da dubu 90 suna sa ido kan dandalin nune-nune, yarinya kurma mai shekaru 10 da haihuwa Wang Yimei ta zuba ido kan babbar wutar yola, ta yi magana da ita da harshen alamar hannu na duniya, ta ce: "Wutar yola, ko kin san ki yi ta ci a cikin zuciyata? Ko kina ji? Ina rera waka gare ki?" Tamkar babbar wutar yola ta san ma'anar Wang Yimei, kuma ta san za ta ci gaba da ci a cikin zuciyar dukkan 'yan wasa nakasassu, sannu a hankali ne ta lafa. Daga nan, gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ta samu cikakkiyar nasara!

Lubabatu:A cikin kwanaki 11 da suka wuce, 'yan wasa nakasassu fiye da dubu 4 da suka zo daga wurare daban daban na duniya sun shiga gasanni a manyan fannoni 20, inda suka sami lambobin zinariya 471. Ayyukan da suka yi sun nuna mana tunanin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, wato "nuna ficewa da haduwa da kuma morewa"

Lawal:A idanun nakasassu, wasannin motsa jiki ba kawai su iya kawo musu lambobin zinariya da kuma mutunci ba, har ma suna iya kawo musu jaruntaka da kuma aniya. A farkon watan Mayu na shekarar da muke ciki, mahaukaciyar guguwa ta Nargis ta kai hari ga kasar Myanmar. Dan wasa Winn Niang na Myanmar da ya shiga gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing yana zama a daidai wuraren da suka fi fama da wannan mummunan bala'i. Wasu danginsa sun rasu a sakamakon wannan bala'i, shi ma ya ji rauni. Winn Niang ya bayyana cewa, ya jure wahalhalu iri daban daban ya zo nan Beijing domin shiga gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Dalilin da ya sa haka shi ne domin ya sami jaruntaka daga wajen wasannin motsa jiki.

"Ina tsammani na sami sa'a. Wasannin motsa jiki sun kawo mini farin ciki da jin dadi sosai, sun kuma ba ni jaruntaka in ci gaba da zaman rayuwata. Na nemi samun lambar yabo ne domin kawo wa mahaifata kasar Myanmar mutunci, haka kuma shi ne burina. In na iya shiga gasanni, to, zan ci gaba da aikin horaswa."

Lawal:Kafin shekaru 7, Beijing ya taba yin alkawari cewa, "za a shirya gasanni Olympic biyu gaba daya, kuma dukkansu za su kayatar sosai", bayan shekaru 7, Beijing ya cika alkawarinsa kan ayyukan da ya yi a zahiri. Game da gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing, Mr. Philip Craven shugaban kwamitin wasannin Olympic ta nakasassu na duniya ya ce, "Wannan wani al'amari ne mai ma'anar tarihin gasar Olympic ta nakasassu. Muna jin dadin hakan."

1 2 3 4 5 6