Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-17 22:23:45    
An rufe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing

cri

Lawal:"Wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu gagarumin biki ne da ya bayyana tunanin yin fice da haduwa da morewa. 'Yan wasa nakasassu fiye da dubu 4 na kasashe da yankuna 147 sun yi kokarinsu na neman cigaba da kwazo da himma a gun gasar, inda suka kara matsayin bajinta na duniya har sau 279 tare da matsayin bajinta na gasannin wasannin Olympic na nakasassu 339. Sun kafa kyawawan maki masu girmamawa, sun kuma bayyana yadda suke neman cigaba da kansu da yin zama da kansu tare da mutunci da imani, har ma kamar yadda suke rera wakar yaba wa rayuka. Wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu gagarumin biki ne da ke kulawa da ciyar da harkokin nasakasassu gaba. Ta hanyar shirya wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu, ba ma kawai an kyautata aikin samar da ayyuka marasa shinge ba, har ma an kafa wata gadar da ke bayyana cewa babu shinge tsakanin nakasassu da masu lafiya."

Lubabatu:A gun bikin rufe gasar, shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya wanda ke zaune a cikin keken guragu Philip Craven ya karbi wani ganye mai launin ja daga kasa, ya sa ganyen a cikin aljihunsa, wannan ya alamanta cewa, ya riga ya karbi fatan alherin da dukkan jama'ar kasar Sin ke nuna wa gasar wasannin Olympic ta nakasassu. Daga baya kuma ya bayar da wani rahoto mai cike da kuzari wanda ke da lakabin haka: "Wasika ga lokacin gaba".

Lawal:"Wannan ne wani gagarumin biki kwarai. Bikin kaddamar da gasar da ba a safai a kan gani ba. Dakuna da filaye na motsa jiki dukkansu suna da inganci da kyaun gani. Ana jin mamaki sosai ga matsayin da 'yan wasa suke dauka. Kuma ba a taba ganin irin wannan kyakkyawan sharadin unguwar 'yan wasa ta nakasassu ba a da. An kuma share fage da shirya wannan gasa da kyau kwarai da gaske. Masu aikin sa kai ma sun yi namijin kokari. Dubban masu sha'awar wasannin motsa jiki na nakasassu sun bullo a nan kasar Sin, har ma a duk duniya. Wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu wata gasar wasannin Olympic ta nakasassu ce da ta fi kayatarwa a tarihi."

Lubabatu:A gun bikin, an ba da lambar yabo ta mafi yin kokari wadda ke fin nuna mana halin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ga Said Gomez, wani dan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Panama da Natalie du Toit, 'yar wasan ninkaya ta kasar Afirka ta kudu.

1 2 3 4 5 6