Lawal:Assalamu alaikum! Jama'a masu sauraro, barkanmu da saduwa da ku a shirinmu na musamman game da bikin rufe gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, kuma ni ne Lawal tare kuma da Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.
Lawal: Masu sauraro, wakar da kuke saurara waka ce ta kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya. Yau wato ran 17 ga wata da dare, agogon Beijing, an sake rera wannan waka a filin wasan motsa jiki na kasar Sin da ake kira shi "Shekar Tsuntsu", wannan ya almanta cewa, an kawo karshen gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta shekarar 2008 da aka shafe kwanaki 11 ana yinta a Beijing.
Lubabatu:A cikin kwanaki 11 da suka shige, 'yan wasa sama da 4000 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 147 sun nuna mana halayensu na kwazo da himma da kishin zaman rayuwa da kuma wucewa karfinsu bisa babban batun gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing wato "yin ficewa da haduwa da kuma morewa", ana iya cewa, suna jin dadin kuzari da farin cikin da wasannin ke kawo musu, a sa'i daya kuma, jama'ar kasashen duniya masu lafiya su ma suna jin dadin nune-nunensu, ana jin mamakin karfin halin da 'yan wasa nakasassu ke nunawa. Bari mu nuna babbar biyayya ga 'yan wasa wadanda ke nuna mana abin mamaki na dan adam.
Lawal:Yau da dare, an tuna da kwanaki 11 da suka wuce ta hanyar shirya bikin rufe gasar wasannin Olympic ta nakasassu mai cike da soyayya. Kamar yadda kuka sani, jan ganye na dutsen 'Xiangshan' da ke nan birnin Beijing shi ne alamar fasalin kaka na Beijing, shi ya sa an yi amfani da ganye na launin ja a gun bikin rufe gasar domin nuna fatan alheri na jama'ar kasar Sin ga aminai nakasassu na duk fadin duniya. Muna fatan za su kara yin kokari domin jin dadin zaman rayuwa.
Lubabatu:Shugaban kasar Sin Hu Jintao da shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya Philip Craven da shugaban kwamitin wasannin Olympic na duniya Jacques Rogge da manyan baki daga kasashe 20 sun halarci bikin.
A gun bikin rufe gasar, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing Liu Qi ya yi jawabi wanda ke da lakabin haka: "Fatan alheri daga ganye mai launin ja na dutsen 'Xiangshan'".
1 2 3 4 5 6
|