Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Cutar COVID-19 ta haddasa illa ga fannin kiwon lafiyar Afirka
2020-11-06 14:29:16        cri
Jiya Alhamis, ofishin kula da harkokin Afirka na hukumar kiwon lafiyar duniya ta WHO, ya bayyana cewa, yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, ta haifar da babbar barazana ga aikin ba da hidima a fannin kiwon lafiya na nahiyar Afirka.

WHO ta fidda wannan bayani ne, bayan nazarin da ta yi kan harkokin kiwon lafiya da suka hada da samar da jinya, da samun kulawa a asibiti, da aikin unguzoma, da kuma jinyar ciwon zazzabin cizon sauro da dai sauransu.

Daga watan Janairu zuwa watan Satumba na bana, hukumar ta yi bincike a kasashe guda 14, cikin wadannan kasashe, aikin ba da hidima a fannin kiwon lafiya ya ragu sosai, idan aka kwatanta da yadda aka aiwatar da wannan aiki cikin shekaru biyu da suka gabata.

Haka kuma, an ce, daga watan Janairu zuwa watan Agusta na bana, yara a nahiyar Afirka kimanin miliyan 1.37 sun kasa samun allurar rigakafin tibi, kana, yaran da ba su kai shekara daya ba, su kimanin miliyan 1.32 sun kasa samun allurar rigakafin kyanda. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China