Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoto: Zaman lafiyar Afrika na janyo hankalin masu zuba jari yayin da duniya ke fama da rashin tabbas
2020-11-06 09:44:37        cri

Wani rahoto da aka fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa, sauye sauyen siyasa yana janyo jarin kai tsaye na kasashen waje zuwa Afrika.

Rahoton wanda Jersey Finance, wani kamfanin kula da harkokin kudi ne na Afrika ta Kudu, ya bayyana cewa, yayin da ake samun karuwar daidaituwar tsarin tafiyar da kudade a Afrika, akwai karuwar damammaki masu alfanu a nahiyar kuma ya sha banban da hasashen yiwuwar fuskantar matsaloli wanda wasu kasashen yammacin duniya suka yi yayin da nahiyar ke cigaba da neman fadada hanyoyin samun kudaden shiga.

Rahoton ya nuna cewa, masu zuba jari suna kokarin neman mafaka domin kaucewa samun sakamako maras tabbas daga ficewar Birtaniya daga tarayyar Turai wato Brexit da kuma annobar COVID-19, a cewar rahoton yanzu masu zuba jari suna neman hukumomi ne masu inganci da gudanar da al'amurra a bayyane, gami da dokoki masu karfi.

Sannan rahoton ya nuna cewa annobar COVID-19 ta yi matukar mayar da hannun agogo baya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China