2020-11-06 12:37:40 cri |
Hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta bayyana a jiya Alhamis cewa, sama da mutane miliyan 600 dake zaune a sassa daban-daban na nahiyar Afirka ba su iya samun hasken wutar lantarki, duk da tarin albarkatun makamashin da ake iya sabuntawa dake jibge a nahiyar.
Kwamishinan kungiyar AU mai kula da kayayyakin more rayuwa da makamashi, Amani Abou-Zeid ne ya bayyana haka, yayin wani taron samar da wutar lantarki bisa tururi (ARGeo-C8), taron da ya hallara masana daga sassan samar da wutar lantarki bisa karfin tururi, da tsoffin shugabannin kasashe da mambobin kungiyar samar da makamashi bisa karfin tururi daga sassan Afirka, da Turai da Asiya, a wani mataki na samar da kimanin MW 20,000 na makamashi bisa tururi a Afirka.
Ya ce, manufar taron ita ce bunkasa da goyon bayan raya fasahar samar da makamashi bisa karfin tururi a yankin gabashin Afirka.
Cikin wadanda suka halarci taron na kasa da kasa, sun hada da masu tsara manufofi, da masana a fannin tsare-tsare da masu tsara matakan ci gaba da masu daukar nauyin wakilai na kasa da kasa da na shiyya-shiyya.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China