Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron kiwon lafiya na duniya
2019-05-21 13:20:14        cri

A jiya ne, aka bude taron kiwon lafiya na duniya karo na 72 a birnin Geneva, inda aka tattauna batun "tabbatar da lafiya ga kowa da kowa", da sa kaimi ga kasa da kasa da su dauki matakai don cimma wannan buri.

A jawabinsa yayin taron, direktan hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, kasashen duniya za su iya gano tare da magance cututtukan da ba za su bazuwa ta hanyar daukar matakan kiwon lafiya, matakin dai a magance cututtukan da ake gamu da su ba zato ba tsammani har daga karshe su zama masu tsanani.

Za a gudanar da taron kiwon lafiya na duniya a wannan karo ne tun daga ranar 20 zuwa 28 ga wannan wata. Bisa ajendar taron, ban da batun kiwon lafiya, za kuma a tattauna batutuwan samar da magunguna da allurar rigakafi da dai sauransu. Kana za a maida hankali ga batutuwan farashin magunguna da allurar rigakafi da sauran kayayyakin kiwon lafiya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China