Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Likitoci Sinawa da suka yi aikin yaki da COVID-19 a Lesotho da Angola sun dawo gida
2020-11-06 12:42:17        cri

Jiya ne wata tawagar likitoci Sinawa mai mutane 10, suka dawo lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin, bayan shafe kwanaki 25 suna taimakawa ma'aikatan lafiya a kasashen Lesotho da Angola, dabarun yaki da cutar COVID-19.

Ita dai wannan tawaga dake karkashin hukumar lafiya ta kasar Sin, ta kunshi ma'aikatan lafiya na lardin Hubei da suka kasance a kan gaba wajen yaki da wannan annoba.

Masanan sun kware ne a fannonin shakar numfashi, da matsananin hali na jinya, da cututtuka masu yaduwa, da magungunan gargajiya na kasar Sin, da kare yaduwar cututtuka.

Shugaban tawagar kana mataimakain shugaban Asibitin Tongji dake Wuhan Liu Zheng, ya bayyana cewa, tawagar ta raba fasahohinta na kula da marasa lafiya, da kare yaduwar annoba a cikin al'umma, da kwarewa a fannin gwajin cutar ga takwarorinta na kasashen Lesotho da Angola.

Haka kuma masanan, sun horas da ma'aikatan lafiya, da masu aikin kare yaduwar cututtuka a cikin al'umma, gami da Sinawa dake aiki da kuma zama a wadannan kasashe, dabarun kare kansu daga kamuwa da kwayar cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China