Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta yi musayar kwarewa a fannin kiwon lafiya a taron lafiya na kasa da kasa
2019-05-19 15:42:38        cri
Kasar Sin za ta yi musayar kwarewar da ta samu cikin gwamman shekaru a fannin ayyukan kula da lafiya matakin farko a lokacin babban taro kiwon lafiya na duniya wato (WHA), dake tafe, wanda taron zai mayar da hankali kan tsare-tsare da manufofi da suka shafi kula da lafiyar al'umma a matakin farko, wakilin kasar Sin dake halartar taron na WHA ne ya bayyana hakan a Geneva a ranar Asabar.

Sama da komai, kwarewar kasar Sin ta samu ne sakamakon yadda gwamnatin Sin take mayar da hankali game da lafiyar al'umma a matsayin muhimmin jigo, kana da bada fifiko kan dabarun kiwon lafiyar al'umma a matsayin wani bangare na bunkasa ci gaban kasa, Nie Chunlei, shugaban sashen kula da lafiya matakin farko na hukumar lafiyar kasar Sin, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai, gabanin taron na WHA karo 72.

Kasar Sin ta gabatar da cikakken tsari game da shirin raya kiwon lafiya mai taken "Healthy China 2030" tun a shekarar 2016, inda shirin lafiyar na kasar Sin ya yi hadaka ya koma wani cikakken shirin lafiya na kasa domin tabbatar da cimma nasarar muradin samun dawwamamen ci gaba, in ji shi. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China