2020-08-31 19:59:50 cri |
Da yake karin haske kan kalaman da Pompe ya yi cewa, wai kasar Sin ce ke da kusan kaso 30 cikin 100 na tarkacen robobin da ake zubarwa a duniya. Zhao ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci kan batun da ya shafi kare muhalli, tana kuma daukar kyakkyawan muhallin halittu a matsayin batu mafi fa'ida ga rayuwar jama'a, ta kuma bayar da gagarumar gudummawa wajen kare muhalli, da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli gami da ci gaba mai dorewa.
Haka kuma, kasar Sin ta cika alkawuran da ta dauka game da wannan yarjejeniya, ta kuma ba da babbar gudummawa kan yadda ake tafiyar da harkokin da suka shafi muhalli a duniya. A hannu guda kuma, a matsayin Amurka na kasar dake kan gaba wajen fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, kana kasar take kan gaba wajen fitar da shara da ma robobi a duniya zuwa ketare, wadanne matakai Amurkar take dauka wajen kare muhalli? A fili yake cewa, an san wadda ba ta damu da muhallin duniya da ma lafiyar al'ummar duniya baki daya ba. (Ibrahim Yaya)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China