Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zhao Lijian: Ba ruwan sassan waje da batun yankin HK
2020-08-12 20:09:25        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce majalissar dokokin HK, za ta ci gaba da aiki bisa doka, kuma harkar zaben 'yan majalissun yankin, batu ne da ya shafi zabe irin na cikin gidan kasar Sin.

Zhao Lijian ya yi wannan tsokaci ne, yayin taron manema labarai na rana rana a yau Laraba. Ya kuma jaddada cewa, harkokin yankin HK, harkoki ne na cikin gidan kasar Sin, da bai dace gwamnatin wata kasa ta waje, ko wasu hukumomi, ko ma daidaikun mutane su tsoma baki cikin su ba.

Da ya tabo batun alakar Sin da kasar Amurka, Zhao Lijian ya ce kasashen biyu, na da damar yin cudanya, tare da martaba juna a ko wane mataki, duk da cewa, da ma tuni suna gudanar da shawarwari.

Game da batun tsokacin da sakataren lafiyar kasar Amurka ya yi don gane da matakan Sin na yaki da cutar COVID-19 kuwa, Zhao ya ce, kamata ya yi sakataren ya yi watsi da batun siyasa, ya mayar da hankali ga kare rayukan Amurkawa, wanda hakan ne nauyin dake wuyan sa.

Da aka tabo batun manhajar Tik Tok kuwa, Zhao Lijian ya ce, akwai wasu mutane Amurkawa dake yin duk yadda suke so, domin biyan bukatun kashin kansu, to sai dai kuma, alhakin kuskuren su zai koma ne gare su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China