![]() |
|
2020-08-10 20:51:47 cri |
Da yake tsokaci game da hakan, yayin taron manema labarai da ya gudana a Litinin din nan, kakakin ma'aikatar wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Sin ta kakaba takunkumin ne kan wasu Amurkawa, da suka hada da Sanata Marco Rubio, da Ted Cruz, da Josh Hawley, da Tom Cotton, da Pat Toomey, da sauran su, duba da kasancewar su masu hannu dumu dumu a sha'anin tsoma baki cikin batun yankin HK.
A ran 7 ga watan, Amurka dai ta fake da cewa, ta ayyana matakin kakaba takunkumi ga wasu manyan jami'an kasar Sin da na yankin HK ne, sakamakon zargin su da yiwa manufar cin gashin kan yankin Hong Kong kafar ungulu.
To sai dai kuma Mr. Zhao Lijian ya ce, matakan da Amurka ta dauka sun zamo tsoma baki dumu-dumu cikin harkokin yankin HK, da shiga sharo ba shanu cikin harkokin gidan kasar Sin, wanda hakan ya yi matukar keta hurumin dokokin cudanyar kasa da kasa, da ka'idojin alakar kasashen duniya da aka amince da su. Don haka Sin na matukar adawa da matakan na Amurka. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China