Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Maikatan karamin ofishin jakadancin Sin dake Houston sun sauka birnin Beijing
2020-08-18 09:59:11        cri

Ma'aikatan karamin ofishin jakadancin Sin dake birnin Houston na Amurka da aka rufe, sun sauka filin jiragen sama na birnin Beijing da yammacin jiya Litnin, inda suka samu tarba daga dan majalissar gudanarwar Sin kana ministan wajen kasar Wang Yi.

Jami'an sun iso kasar Sin ne a jiya, baya an rufe karamin ofishin jakadancin na Houston, da dakatar da dukkanin ayyukansa da gwamnatin Amurka ta yi a ranar 21 ga watan Yulin da ya gabata.

Cikin sakon maraba da ya gabatar, Wang ya jinjinawa jami'an ofishin da aka rufe, yana mai cewa duk da yanayi na ba zata da aka fuskanta, ma'aikatan su kai zuciya nesa, tare da kwantar da hankulan su, sun kuma kare moriyar kasar su, da kima da mutuncin al'ummar ta. Kaza lika sun kiyaye hakki da bukatun hukumomin kasar Sin dake ketare a wannan mawuyacin lokaci, da ma muhalli mai hadari.

Mr. Wang ya kara da cewa, karamin ofishin jakadancin Sin dake Houston ya nuna wa duniya mummunan tasirin dake tattare da aiwatar da matakan gurgunta alakar Sin da Amurka, da burin wasu sassa na darkushe ci gaban kasar Sin da gangan. To sai dai kuma Wang ya ce tarihi zai fayyace kuskuren masu wannan aniya, kana yunkurinsu ba zai yi nasara ba.

Daga nan sai ministan ya sake jaddada fatan kasar Sin, na ganin farfadowar dangantakar Sin da Amurka, bayan wucewar wannan yanayi mai tsanani da ake ciki, yana mai cewa, makomar kasar Sin na hannun al'ummar ta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China