Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin ta soki ziyarar da sakataren lafiyar Amurka ya kai Taiwan
2020-08-10 20:12:14        cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi kakkausan suka, game da ziyarar da sakataren lafiya da samar da hidimomi ga jama'ar Amurka Alex Azar ya kai yankin Taiwan na Sin. Ma'aikatar ta kuma bukaci Amurka, da ta daina gudanar da kowace irin cudanyar jami'ai tsakaninta da Taiwan, ta kuma kauracewa daga matsayin dangantaka da tsibirin, wanda bangare ne na kasar Sin.

Da yake bayyana hakan, yayin taron manema labarai da ya gudana a Litinin din nan a birnin Beijing, bayan gabatar masa tambaya don gane da ziyarar Mr. Azar, kakakin ma'aikatar Zhao Lijian, ya ce batun Taiwan daya ne daga manyan batutuwa masu shafar dangantakar Sin da Amurka, yayin da kuma batun manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya ke kan gaba, kasancewar sa ginshikin dangantakar siyasa tsakanin sassan biyu.

Mr. Zhao ya kara da cewa, matakin Amurka na tura jami'ai yankin Taiwan, ya sabawa alkawarin da ta yi, game da matsayin yankin na Taiwan. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China