Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Sin: Neman lalata dangantaka tsakanin kasashe ba zai haifar da da mai ido ba
2020-08-25 11:31:26        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce duk wani yunkurin da wata kasa za ta yi na neman lalata dangantakar dake wanzuwa a tsakanin kasashen duniya ya saba dokokin kasuwanci da tattalin arziki da muradun kamfanoni, kuma lamarin zai iya zama tamkar kaikayi ne dake iya komawa kan mashekiya.

Wang, ya yi wannan tsokaci ne a yayin da yake zantawa da 'yan jiridu bayan kammala tattaunawa da ministan harkokin wajen kasar Hungry, Peter Szijjarto, a Beihai na yankin Guangxi Zhuang mai cin gashin kai.

Da yake mayar da martani game da tambayar da aka yi masa kan batun takunkumin da Amurka ta sanyawa wasu kamfanonin kasar Sin, da kuma yunkurinta na neman lalata dangantaka da Sin, Wang ya ce, wannan batun neman yanke alakar ba shi da tabbaci, kuma babu hikima cikinsa, kana duk wani yunkurin neman lalata dangantakar siyasa babu abin da zai haifar illa koma baya ga ci gaban ita kanta Amurkar da kuma lalata moriyar jama'arta. Yunkurin ba zai yi nasara ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China