Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Sin ya bayyana matsayin kasar Sin kan dangantakar Sin da Amurka
2020-08-06 11:18:19        cri

A ranar Laraba ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi muhimmiyar tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua game da batutuwan dake shafar dangantaka tsakanin Sin da Amurka.

Yayin tattaunawar Mr. Wang ya jaddada cewa, Hong Kong wani bangare ne na kasar Sin kana al'amurran da suka shafi Hong Kong batu ne na cikin gidan kasar Sin. Kaucewa yin shisshigi a al'amurran cikin gidan kasashe muhimmin batu ne a tsarin dangantakar kasa da kasa, kuma babu wata kasa da za ta taba lamintar yi mata zagon kasa game da ikonta ko kuma wasu yankunanta daga wasu kasashen duniya.

Duk wani shisshigi game da harkokin Hong Kong, ko yin wasu kalamai ko kuma aikata wani abu, babu abin da hakan zai haifar sai neman gurgunta manufar nan ta "kasa daya amma tsarin mulkin iri biyu", kuma dukkan al'ummar Sinawa, ciki har da mutanen yankin Hong Kong ba za su taba lamintar hakan ba.

Yana mai cewa, Amurka tana shirya makarkashiya a dukkan sassan duniya, kuma wannan mummuna aiki da take aikatawa wani sirri ne wanda tuni an riga an gano shi, Wang Yi ya ce, Amurka ba ta cancanci jagorantar gina duk wata hadaka mai tsabta a tsakanin kasashe ba, saboda babu tsafta a tattare da ita. Kasar Sin za ta ci gaba da yin aiki tare da dukkan kasashen duniya domin tabbatar da adalci, da yin al'amurra babu rufa-rufa, kuma ba tare da nuna wariya ba a tsarin samar da muhallin kasuwanci, kuma za ta tabbatar da samun tabbaci, da samar da ingantattun fasahohin zamani wadanda za su bunkasa farfadowar tattalin arzikin duniya, da kyautata zaman rayuwar al'ummar kasa da kasa.

Minista Wang Yi ya jaddada cewa, ya kamata Sin da Amurka su dakatar da duk wani yunkurin samar da baraka, kana su yi kokarin karfafa dangantakar dake tsakaninsu ta hanayar hadin gwiwa, kuma su yi kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu na kasa da kasa. Ya kara da cewa, dukkan kasashen biyu sun amfana matuka daga hadin gwiwar dake tsakaninsu, kuma babu wani bangare dake ci da gumin wani bangare, kasancewar mu'amalar cin moriyar juna da suka shafe tsawon shekaru suna gudanarwa ta baiwa kasashen Sin da Amurka damar samun babbar moriya ga al'ummominsu.

Wang Yi ya karfafa cewa, kasar Sin ba ta da wata niyya ko burin yin shissshigi cikin harkokin zaben kasar Amurka, ko kuma al'amurran cikin gidan kasar. Ya kamata Amurka ta guji aikata duk wani abu da zai lahantar moriyar kasar Sin da ci gabanta, ta kaucewa yin katsalandan a harkokin cikin gidan kasar Sin ba bisa ka'ida ba, kana ta guji aikata duk wani abu da ya keta hurumin kasar Sin wanda zai lahanta moriyarta.

Game da batun yankin tekun kudancin kasar Sin, minista Wang Yi ya sake nanata cewa, yankin bangare ne dake shafar kasashen dake shiyyar, bai kamata a mayar da shi wani bangare na siyasar duniya ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China