Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Danginku kuma dangi ne na jamaar kasa
2020-08-20 13:55:12        cri

Da yammacin ranar 19 ga watan Ogusta, Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, wanda ke ziyarar aiki a lardin Anhui, ya ziyarci sashen tafkin Chaohu dake yankin Feidong, na birnin Hefei. Xi Jinping ya kai ziyara tare da yin ta'aziyya ga iyalan Chen Lu da sauran mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin da suke bakin aikin yaki da ambaliyar ruwa.

Xi Jinping ya ce: "Danginku kuma danginmu ne, kuma dangin jama'ar kasarmu ne. Kuma sun kasance jarumai da ba za mu taba mantawa da su a cikin zuciyarmu ba. A lokacin da kasar Sin ta shiga cikin bala'i, ana samun irin wadannan jarumai dake sadaukar da kansu. Wadannan su ne ruhin kasarmu. Dukkanmu za mu mutunta su. Muna fata za ku tuna da su ta hanya mafi dacewa, ku tsara yanayin aikinku, rayuwarku, da kiyaye lafiyar jiki domin kwantar musu da hankali." (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China