Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya ziyarci birnin Hefei na lardin Anhui
2020-08-20 09:21:30        cri

 

Babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping, ya ziyarci birnin Hefei, fadar mulkin lardin Anhui dake gabashin kasar da yammacin jiya Laraba.

Yayin wannan ziyara, shugaba Xi ya duba wani sashe na madatsar ruwa dake gundumar Feidong, inda ya ganewa idanun sa yanayin gudanar tafkin Chaohu, ya kuma jinjinawa masu aikin yaki da ambaliyar ruwa a yankin, wadanda suka kunshi dakarun sojin kasar Sin na PLA, da kuma rukunin 'yan sanda masu dauke da makamai.

Shugaban na Sin ya kuma kai ziyara cibiyar kirkire kirkire ta Anhui, don ganin yadda ake bunkasa fasahohin kirkire kirkire, da raya sabbin masana'antu a lardin Anhui.

Kaza lika ya halarci dakin nune-nune na tunawa da gangamin ratsa kogin Yangtze da rundunar PLA ta gudanar, yayin yakin kwatar 'yancin al'ummar kasar, inda ya bayyana alhinin rayukan 'yan mazan jiya da suka kwanta dama a lokacin wannan yaki. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China