2020-08-17 20:24:37 cri |
Haka kuma, Zhao Lijian ya ce, wasu 'yan siyasan kasar Amurka suna daukar batun "kare tsaron kasa" a matsayin hujjar matsawa kamfanonin da ba na kasar Amurka ba lamba a ko da yaushe. Gwamnatin kasar Amurka ta ce, kamfanin ByteDance na Sin da ya kirkiri manhajar TikTok, da sauran wasu kamfanoni suna kalubalantar tsaron kasar Amurka, amma, hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta CIA ba ta gano shaidun da suka nuna cewa, kasar Sin ta saci bayanan TikTok, ko kuma yin amfani da manhajar TikTok wajen satar bayanai daga wayoyin salulan jama'a ba. Bugu da kari, wasu kwararrun kasar Amurka sun nuna cewa, yadda kasar Amurka ta hana amfani da manhajar TikTok saboda na kasar Sin ne, bai shafi batun kare tsaron kasa ko kadan ba. (Maryam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China