Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jagororin Sin da Amurka dake tattaunawar cinikayya sun zanta ta wayar tarho
2019-11-26 13:59:43        cri
Mataimakin firaministan kasar Sin, kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, kana jagoran tawagar Sin dake tattauna harkokin cinikayya da Amurka wato Liu He, ya zanta ta wayar tarho da wakilin Amurka kan harkokin cinikayya, Robert Lighthizer da kuma sakataren baitulmalin Amurkar Steven Mnuchin, da safiyar yau Talata.

Bangarorin biyu sun tattauna kan warware batutuwan dake ciwa kowanne bangare tuwo a kwarya da cimma matsaya kan warware batutuwan da kuma amincewa da ci gaba da tattaunawa kan sauran batutuwa bisa tuntuba, a matakin farko na cimma yarjejeniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China