2020-08-15 19:51:15 cri |
Kwanan baya, darektan kwamitin ciniki na fadar White House, Peter Navarro, ya shedawa wakilin FOX News cewa, ya shiga rudani game da fusatar da Amurkawa suke nunawa gwamnatin game da barakar da cutar COVID-19 ta kawowa al'ummar kasar. Har ya yi nazari bisa tunanin da ya dade yana da shi cewa, idan Amurkawa sun dora laifi kan Sinawa, to al'ummar za ta samu farfadowa daga cutar. Irin wannan magana maras imani da ya fadi ya girgiza mai jagorancin shiri da ma masu kallo matuka. Ana iya ganin cewa, Peter Navarro ya fadi abubuwa yadda yake so maras ma'ana don dora laifi kan kasar Sin ta yadda za a gudun sauke nauyin dake wuyan gwamnatin na gaza daukar matakan da suka dace don yakar cutar.
An lura cewa, kwanaki biyu gabanin zantawa da Peter Navarro, yawan mutanen da cutar ta harba ya kai fiye da mililyan 5 a kasar, yawan mamata kuma ya kai dubu 162.8. Hakikanin halin da Amurka ke ciki na cin tura wajen hana yaduwar cutar da ma kusantowar babban zaben kasar, shi ne dalilin da ya sa Peter Navarro ya yi irin wannan wasan kwaikwayon, a sa'i daya kuma, ta wannan hanya yana nufin cimma wani boyayen buri a siyasance.
Tedros Adhanom Ghebreyesus babban sakataren WHO ya taba yin kira ga kasashen duniya ba da dadewa ba bayan bullowar cutar cewa, kamata ya yi kasashen duniya su hada kansu. Amma, 'yan siyasar Amurka sun nuna ko in kula ga wannan kira, har ma sun dora laifi kan sauran kasashe don cimma burinsu a siyasance.
Kwanan baya, darektan hukumar CDC ta Amurka, Robert Redfield, ya yi gargadi yayin da ya zanta da manema labarai cewa, idan ba a nace ga manufar sanya marufin baki da hanci da nisantar da juna ba, yanayin kasar a wannan karo a lokacin kaka mai zuwa zai zama lokaci mafi muni a tarihi. Abin da ya fi jawo damuwar mutane shi ne, irin magana maras kyau da Peter Navarro ya yi inda ya nuna cewa, tsarin tsaida manufofi da Amurka ta dade tana kai wata hanya ce ta kuskure, gwamnatin ba ta maida hankali kan cutar ba ko kadan.
Abubuwan da Peter Navarro ke yi ba ma kawai ya bayyana matsayin jami'an White House maras imani da mutunci ba ne, har ma ya zama abin ban dariya ne a tarihin siyasar kasar. Amma, 'yan siyasa iri su Peter Navarro suna da yawa a Amurka, abin da ya fi ta da zukatan mutane. A matsayinta na kasa mafi karfi a duniya, Amurka tana da tushe mai inganci wajen tinkarar wannan cutar, amma saboda matakai marasa kyau da gwamnatin ke dauka ya jefa jama'arta cikin mawuyacin hali. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China