Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an lafiyar Amurka sun nuna damuwa game da canza tsarin fitar da bayanan annobar COVID-19 a kasar
2020-08-15 16:18:31        cri
Kungiyar jami'an kiwon lafiya masu ba da shawara ga gwamnatin kasar Amurka sun bayyana damuwarsu game da yadda gwamnatin Trump ta dauki matakin sauya salon yadda asibitoci ke fitar da alkaluman bayanan cutar COVID-19 a kasar, kafar yada labaran CNN ce ta bada rahoton a ranar Juma'a.

Gwamman mambobin kwamitin bada shawara kan dakile cutuka ne suka bayyana damuwarsu cikin wata wasika da suka aika zuwa ga sashen hukumar kula da al'amurran lafiya ta Amurka HHS, kamar yadda CNN ta wallafa a shafinta na intanet.

Hukumar lafiyar ta HHS ta wallafa wasu bayanai a shafinta na intanet a watan jiya, tana mai cewa, gwamnatin Trump ta umarci asibitocin kasar da su bayar da dukkan wasu bayanan dake shafar masu fama da cutar COVID-19 zuwa ga hukumar HHS, a maimakon bayar da bayanan ga hukumomin HHS da CDC da aka saba yi a lokutan baya.

Tsohon daraktan hukumar CDC, Richard Besser ya ce wannan sauyin da aka yi babban koma baya ne ga shirin yaki da annobar COVID-19 a Amurka, kuma hakan tamkar an mayar da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta CDC 'yan kallo ce. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China