Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Amurka: Sabon yakin cacar baki da Amurka take son tadawa tsakaninta da Sin, zai fi cutar COVID-19 haddasa karin barazana ga kasashen duniya
2020-06-22 11:07:23        cri

Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na BBC na kasar Burtaniya ya fidda, masanin tattalin arzikin kasar Amurka, kana, shugaban cibiyar neman dauwamammen ci gaba ta jami'ar Columbia, Jeffrey Sachs ya ce, gwamnatin dake karkashin jagorancin Donald Trump tana son tada sabon yakin cacar baki tsakanin Amurka da kasar Sin, wanda zai haddasa karin barazana ga kasa da kasa, idan aka kwatanta da matsalolin da cutar COVID-19 ta haifar ga kasashen duniya.

Malam Sachs ya soki matakan kiyayya da gwamnatin kasar Amurka ta dauka kan kasar Sin. Ya ce, Amurka tana son rabuwa a maimakon hadin gwiwa, akwai wasu dake son tada sabon yakin cacar baki tsakanin kasar Amurka da kasar Sin. Idan Amurka ta ci gaba da daukar irin wadannan matakai, ba za a samu farfadowa ba, sai ma fuskantar karin barazana.

Ban da haka kuma, da yake tsokaci kan takunkumin da kasar Amurka ta kakaba wa kasar Sin, musamman ma babban kamfanin sadarwa na Huawei na kasar Sin, malam Sachs ya bayyana cewa, kasar Amurka ta kakaba wa kamfanin Huawei takunkumi, ba kawai domin batun kare tsaron kasa ba, har ma da matsayi na daya da kasar Sin ta samu a fannin fasahar 5G, wadda ta kasance muhimmiyar fasaha a fannin raya tattalin arziki ta yanar gizo. A halin yanzu, kamfanin Huawei tana kara bunkasuwa kan wannan aiki a kasashen duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China