Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Apple ya bukaci Amurka da kada ta buga sabon harajin kwastam ga kayayyakin kasar Sin
2019-06-21 16:28:04        cri

Babban kamfanin fasaha na Apple ya bukaci gwamnatin Amurka da kada ta sanya karin sabon harajin kwastam ga kayayyakin da ake shigo da su daga kasar Sin, kamfanin ya ce, sabon karin harajin zai iya rage gudunmawar da kamfanin ke bayarwa ga cigaban tattalin arzikin Amurka, kuma zai iya yin illa game da yanayin takarar kamfanin a kasuwannin kasa da kasa.

A wata wasikar da aka aikewa wakilin hukumar kasuwancin gwamnatin Amurka Robert Lighthizer, wanda aka bayyanawa duniya a ranar Alhamis, mashahurin kamfanin ya bayyana cewa, aniyar da gwamnatin ke da ita na karin harajin kwastam na kashi 25% ga kayayyakin kasar Sin zai yi mummunar illa ga dukkan muhimman kayayyakin da kamfanin ke samarwa, wadanda suka hada da wayoyin iPhone, na'urorin iPad, Mac, AirPods, da kuma AppleTV.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China