Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ba za ta amince da fasfon 'yan Burtaniya mazauna ketare ba
2020-07-23 20:49:12        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana yayin taron manema labarai Alhamis din nan cewa, kasarsa ba za ta amince da fasfon 'yan Burtaniya mazauna ketare, a matsayin halastattun muhimman takardun tafiye-tafiye ba, saboda yadda Burtaniyar ta saba alkawari, kuma tana da 'yancin daukar mataki na gaba.

Gwamnatin Burtaniya dai, ta wallafa bayanai game da tsarin bizar fasfon 'yan kasarta dake ketare (BNO) da take shirin zai fara aiki a farkon shekarar 2021. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China