Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana adawa da matakin Amurka na kafa sansanin kasa na makaman nukiliya na matsakaicin zango a yankunan Asia-Pacific da Turai
2020-08-05 10:51:48        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya sanar a jiya Talata cewa, kasar Sin tana adawa da matakin Amurka na kafa sansanin makamin nukiliya mai cin matsakaicin zango a yankunan Asia-Pacific da Turai.

Ya ce tsokacin da kasar Rasha ta yi game da neman Amurkar ta sauya aniyarta game da soke yarjejeniyar kafa sansanin nukiliya mai matsakaicin zango INF ya kara bayyana hakikanin manufar Amurka.

A ranar Talata ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fidda sanarwa tana mai cewa, matakin da Amurka ta dauka na ficewa daga yarjejeniyar INF shekara guda da ta gabata babban kuskure ne. Ma'aikatar ta kara da cewa, bayan sanarwar janyewar, Amurkar ta gaggauta aiwatar da manufar hana yaduwar makamai wanda a baya aka dakatar saboda yarjejeniyar, hakan ya kara bayyana shirinta na tura manyan makaman nukiliya zuwa yankin Asia-Pacific.

Wang ya ce, bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar INF a hukumance, sai ta cigaba da manufarta na ficewa daga kungiyoyi da yarjejeniyoyi na kasa da kasa, bayan da ta kammala ficewa daga sanya hannu kan yarjejeniyar cinikin makamai, ficewa daga yarjejeniyar ya kara nunawa duniya, matsayinta na kashin kai, hakan yana hanata damar da take da shi game da batun tafiyar da tsarin fasahar makaman nukiliya da batun takaita yaduwar makaman a kasa da kasa.

Ya kara da cewa, har yanzu Amurkar ba ta amince da tsawaita sabuwar yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliyar ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China