Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu wata rufa-rufa a manufar kasar Sin
2020-07-23 20:38:48        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labaran da aka saba shirya kowace rana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin cewa, zargin da kasar Amurka ke yiwa kasar Sin, ya nuna tsarinta na nuna fuska biyu. Yana mai cewa, manufar kasar Sin game da raya hulda tsakanin sojoji da fararen hula, ita ce hade albarkatun sassan biyu waje guda, da raya tattalin arziki da jin dadin jama'a da gina tsaron kasa, da kara kawo wa jama'a nasarorin da aka cimma a fannonin kimiya da fasahar kere-kere. A don haka, karya ne ta soki manufar, kuma babu wata rufa-rufa a ciki. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China