Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kalaman sakataren harkokin wajen Burtaniya kan Xinjiang tamkar bata suna ne
2020-07-20 21:24:05        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron maname labarai a nan birnin Beijing yau Litinin cewa, kalaman bangaren Burtaniya kan yankin Xinjiang, tamkar neman bata sunan kasar Sin ne.

Jami'in na kasar Sin ya bayyana haka ne, yayin da yake mayar da martani kan kalaman baya-bayan da sakataren harkokin wajen Burtaniya Dominic Raab ya yi kan yankin Xinjiang, inda aka ruwaito Rabba na cewa, Burtaniya ba za ta nade hannu tana kallo yadda ake keta hakkin bil-Adama kan kananan kabilu a yankin Xinjiang na kasar Sin ba. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China