Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu baje koli sun kafa kwamitin musammam kan kiwon lafiyar alumma da dakile annoba
2020-07-27 11:00:44        cri

Kungiyar masu baje hajoji na bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin na kasa da kasa CIIE, sun sanar da kafa kwamitoci na musammam a jiya, ciki har da na kula da lafiyar al'umma da kandagarkin annoba.

Masu baje kolin sun yi ammana cewa, kafa kwamitocin na kula da lafiyar al'umma da kandagarkin annoba, na da muhimmanci gaya, yayin da ake yaki da annobar COVID-19.

Bikin CIIE karo na 3, da aka shirya budewa a farkon watan Nuwamba a Shanghai, a karon farko, zai ware wani wuri na musammam domin nune-nunen abubuwan da suka shafi kula da lafiya da kandagarkin annoba. Kusan kamfanoni 50 ne suka nuna sha'awar shiga baje kolin.

Har ila yau a jiya, wasu kamfanoni 35 sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna game da shiga ana damawa da su har na lokaci mai tsawo cikin bikin baje kolin.

Masu baje kolin ne suka kafa kungiyar bayan bikin CIIE na farko da aka yi a shekarar 2018. Yanzu haka, kungiyar na da mambobin 142 daga kasashe da yankuna 23. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China