Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jarin waje na sa ran ga kasuwannin kasar Sin
2020-02-19 11:11:31        cri
Jiya Talata, kamfanin dake karkashin Costco, babban kamfani a duniya wajen sayar da kayayyak, ya yi hadin gwiwa da wani kamfanin kasar Sin, don samun wani fili dake yankin masana'antu na Kangqiao, a sabon yankin Pudong dake birnin Shanghai, bisa kudin Sin RMB har miliyan 898. An ce, za a kafa Costco na biyu a wannan wuri.

An ce, Costco kamfani ne mafi girma a Amurka wajen sayar da kayayyaki, wanda ke da sassa mafi yawa, kuma a shekarar bara, ya shiga kasuwar kasar Sin karo na farko, a yankin Minhang na birnin Shanghai. Shekaran jiya, babban jami'i mai kula da harkokin kudin Costco Richard Galanti, ya bayyana cewa, kamfanin ya yi shirin kafa sassansa na biyu, ya zuwa karshen shekarar 2020, ko farkon shekarar 2021 a birnin Shanghai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China