Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MOC: Yadda bangaren masanaantun samar da kayayyakin Sin ke janyo hankalin jarin waje bai canja ba
2019-11-22 10:51:10        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin Gao Feng, ya bayyana cewa, yadda ake zuba jarin waje a bangaren masana'antun samar da kayayyakin kasar Sin da inganta aikin samar da kayayyaki masu inganci har yanzu bai canja ba.

A hannu guda kuma, raguwar jarin waje da ake zuba wa a wannan fanni a makamancin lokacin bara da aka yi a fanni da shi a watannin 10 na farkon bana, ya faru ne saboda wasu dalilai da ba za a iya kauce musu ba.

Gao Feng ya shaida wa taron manema labarai cewa, daga watan Janairu- Oktoban wannan shekara, jarin waje da aka zuba a bangaren manyan masana'antun zamani, ya karu da kaso 5.5 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara, adadin da ya nuna cewa, an yi amfani da kaso 38.9 cikin 100 na jarin waje a bangaren masana'antun samar da kayayyakin kasar.

A cewarsa, wannan ya nuna yadda ake saurin kaddamar da ayyuka masu jarin waje a cikin kasar da ci gaba da inganta tsarin amfani da jarin waje.

Yana mai cewa, yadda kasar Sin take kokarin bude kasuwanninta, da kafa dokokin inganta yanayin kasuwanci da saukaka harkokin cinikayya da zuba jari, ya nuna yadda take maraba da baki masu sha'awar zuba jari, da su ci gaba da zuba jari tare da hada gwiwa don kara cin gajiyar damammaki da ma nasaraorin bunkasuwar da kasar ta samu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China