Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara daukar matakan tallafawa kamfanoni da tsaron ayyuka
2020-05-07 11:58:47        cri

Majalisar gudanarwar kasar Sin, ta ce kasar za ta kara inganta dabaru da matsa kaimi wajen tallafawa kamfanoni da tsaron ayyuka.

Yayin taron majalisar da ya gudana karkashin firaministan kasar Li Keqiang,an saurari rahotanni kan aiwatar da dabaru da matakan da za su taimaka wajen komawa bakin aiki da samar da kayayyaki da kuma tallafawa kamfanoni.

Sanarwar da majalisar ta fitar, ta ce jimilar dabaru da matakai 90 da suka shafi bangarori 8 ne za a gabatar a aiwatar a kan kari, wadanda za su yi tasiri kan farfado da ayyukan masana'antu da komawa bakin aiki kamar yadda suke a baya, da magance matsalolin kamfanoni da farfado da harkokin tattalin arziki da na zaman takewa.

An kuma tsawaita lokacin biyan bashin harajin na kamfanonin bangarorin yawon shakatawa da sufuri da sayar da abinci daga shekaru 5 zuwa 8.

Sama da ma'aikata miliyan 84 ne suka ci gajiyar dabarun mayar musu da kudin inshorar rashin aikin yi.

Jimilar yuan triliyan 2.85, kwatankwacin dala biliyan 403 na rance mai rangwamen kudin ruwa aka samar ga kanana da matsakaitan kamfanoni da sana'o'i. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China