Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gadoji 20,000 sun zama silar bunkasuwar arzikin Guizhou
2020-07-06 11:13:05        cri

A lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, kaso 92.5% na dukkan yankin tsaunuka ne da duwatsu. Shi ne kadai lardin da babu shimfidaddun filaye a duk kasar Sin. A shekarun baya, rashin hanyoyin sufuri ya yi matukar haifar da koma baya wajen bunkasuwar tattalin arzikin lardin Guizhou, kuma lamarin ya zama tarnaki ga ci gaban tattalin arzikin lardin. Wani karin maganar Sinawa na cewa, "Idan kana son arziki, to ka fara da gina hanya." A shekarun baya bayan nan, lardin Guizhou ya yi nasarar giggina gadoji, lamarin da ya zama tushen samun arzikin yankin.

Wadannan ingantattu da kayatattun gadoji ba ma kawai sun samu yabo daga mazauna wurin ba ne, har ma sun janyo hankalin kasa da kasa. Bisa kididdigar da aka yi, adadin gadojin dake Guizhou ya zarce 20,000, su ne ke da kusan dukkan nau'ikan gadojin da ake da su a duniya a yau. Daga cikin gadoji 100 mafiya shahara a duniya, sama da kashi 80% a kasar Sin suke. Kuma galibinsu suna lardin Guizhou.

Wadannan gadoji daya bayan daya sun zama wasu kayatattun wurare a lardin Guizhou, kuma sun kasance a matsayin wata hanya daya tilo ga ci gaban tattalin arzikin Guizhou, kana sun kasance tushen inganta zaman rayuwar al'ummar yankin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China