Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sanaar aladu da ta yawon shakatawa na ba da babbar gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin Sin
2019-12-25 10:43:46        cri

Bisa kididdigar da ma'aikatar harkokin al'adu da yawon shakatawa ta kasar Sin ta fidda jiya Talata, an ce, cikin watanni 9 na farkon shekarar 2019, kamfanonin dake shafar raya al'adu kimanin dubu 56, sun sami kudin shiga RMB biliyan dubu 62, adadin da ya karu da 7.6% idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.

Jami'in ofishin raya ayyuka na ma'aikatar harkokin al'adu da yawon shakatawa ta kasar Sin Gao Zheng ya bayyana cewa, cikin farkon watanni 9 na bana, akwai mutanen waje sama da miliyan dari 1 da suka zo yawon shakatawa a Sin, adadin da ya karu da 4.7%, kana adadin Sinawa da suka tafi waje domin yawon shakatawa ya kai kimanin miliyan 120, adadin da ya karu da 8.5%.

Ban da haka kuma, a shekarar 2019, kasar Sin ta ba da taimako wajen gudanar da manyan shirye-shiryen hadin gwiwar kasa da kasa, a fannin al'adu da na yawon shakatawa bisa shawarar "ziri daya da hanya daga" guda 85, a kasashe da yankuna guda 20, wadanda suka shafi sana'ar al'adu ta yanar gizo, da sana'ar al'adu da wasan kwaikwayo, da sana'ar na'urorin yawon shakatawa da al'adu da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China