Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Jamhuriyyar Jama'ar kasar Sin halaltacciyar wakiliya ce daya kacal bisa tsarin MDD
2020-05-05 15:49:21        cri

Jami'in hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ya bayyana jiya cewa, jamhuriyyar jama'ar kasar Sin halaltacciyar wakiliya ce daya kacal bisa tsarin MDD, kuma hukumar na bin ra'ayi irin daya da MDD.

Jami'in kula da dokoki na hukumar WHO Steven Solomon ya jaddada a gun taron manema labaru da aka gudanar a cibiyar hukumar a wannan rana cewa, jamhuriyyar jama'ar kasar Sin halaltacciyar wakiliya ce daya kacal bisa tsarin MDD, kuma wannan shi ne kudurin da MDD da hukumar WHO suka tsaida yau shekaru 49 da suka gabata. Ya ce Hukumar WHO hukuma ce dake karkashin tsarin MDD, don haka take bin ra'ayi iri daya da majalisar.

Jami'in ya kara da cewa, za a gudanar da taron kiwon lafiya na duniya karo na 73 ta yanar gizo a ranar 18 ga wannan wata, kuma hukumar WHO tana tsara ajandar taron. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China